Hausa translation of the meaning Page No 237

Quran in Hausa Language - Page no 237 237

Suratul Yusuf from 15 to 22


15. To, a lõkacin ( 1 ) da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, « Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba. »
16. Kuma suka je wa ubansu da dare sunã kũka.
17. Suka ce: « Yã bãbanmu! ( 2 ) Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya! » _
18. Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: « Ã'a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako ( a gunSa ) a kan abin da kuke siffantãwa. »
19. Kuma wani ãyari ( 3 ) ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: « Yã bushãrata! Wannan yãro ne. » Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.
20. Kuma suka sayar ( 4 ) da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.
21. Kuma wanda ya saye shi daga Masar ( 5 ) ya ce wa mãtarsa, « Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã. » Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu,a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. « »
22. Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
( 1 ) Suka cire rĩgarsa, suka jẽfa shi da gũga a cikin rĩjiya. Sa'an nan suka sanya wa rigarsa jinin wata dabba da suka yanka, dõmin ya zama alãmar cẽwa kerkẽci ya cinye Yũsufu. Gã rĩgarsa ta ɓãci da jinin jikinsa, watau jinin shĩ ne alãmar yã mutu. Sai suka manta cẽwa kãfin kerkẽci ya cinye yãroa cikin rĩgarsa, sai yã kekkẽta rĩgar tukun.
( 2 ) Muhãwararsu tãre da ubansu.Yã nũna baƙin ciki, amma kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
( 3 ) Ãyari ya je kusa da rĩjiyar Yũsufu, har suka kãma shi ya zama bãwa abin sayarwa a hannunsu.
( 4 ) Ãyarin, sun tafi da shi, sun sayar da shi a kan kuɗi kaɗan, dõmin sun sani, shĩ bã bãwansu ba ne, tsintõ shi suka yi. Sabõda haka kõme suka sãmu game da shi, rĩba ce agare su. Kuma gudun kada iyãyensa su gãne shi, su rasa kõme daga gare shi gabã ɗaya.
( 5 ) Yũsufu a gidan sarauta, kuma a cikin hãlin girma da ɗaukaka. Gidan Azĩzĩ Masar, watau firãyim Minista, babban wazĩrin Masar.