Hausa translation of the meaning Page No 238

Quran in Hausa Language - Page no 238 238

Suratul Yusuf from 23 to 30


23. Kuma wadda yake ( 1 ) a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, « Yã rage a gare ka! » ya ce: « Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara! »
24. Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.
25. Kuma suka yi tsẽre ( 2 ) zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: « Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi. »
26. Ya ce: « Ita ce ta nẽme ni a kaina. » Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: ( 3 ) « Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata. »
27. « Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya. »
28. Sa'an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: « Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne! »
29. « Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara ( 4 ) dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure. »
30. Kuma waɗansu mãtã ( 5 ) a cikin Birnin suka ce: « Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna. »
( 1 ) Yũsufu yã shiga cikin fitinar uwar ɗãkinsa, zalĩha. Yã mai da al'amarinsa ga Ubangijinsa wanda ya fitar da shi daga rĩjiya zuwa gidan sarautar Masar kuma Ya bã shi hukunci, watau Annabci da ilmi da Ya saukar masa na ibãda damu'amãla. Ya sanar da shi halal da haram kuma ya sanyamasa tsaro daga zunubi.
( 2 ) Idan namiji da mace sun haɗu, to, bã ya halatta ga namijin ya dõgara ga ilminsa na amanarsa, ya zauna tãre da fitinar Shaiɗan. Sabõdahaka Yũsufu ya gudu, ta bĩ Shi da hãlin kãsãwar mutum gahãlin so har bãkin dõfa. Suka haɗu da mijinta. Ta mayar da maganar rawãtsa ( ƙarya ) a kan Yũsufu. Shi kuma ya kãre kansa da maganar gaskiya. Sai shaida zã a nẽma.Tã himmantu da dũkarsa dõmin yã ƙi ya yi mata ɗã'a ga abin da take so daga gare shi alhãli yanã bãwanta, shĩ kuma yã himmantu da dũkarta dõmin ya tunkuɗe macũci. Alfãshar ita ce zina, cũtar kuwa ita ce dũka, dalĩlin Ubangijinsa shĩ ne bin sharĩ' ar Allah.
( 3 ) Bãyar da shaida a kan al'ãda, mai bãyar da shaidar yanã gabãtar da ita da magana a kan Yusufu, dõmin a ganinsa tuhuma a kanta, tã fi karfi, kuma zumuntarsa da ita ba ta ɗauke shi ba ga karkatarda magana dõmin ya taimake ta.
( 4 ) Mai gida ya yi hukunci da yabon girman hãlin Yũsufu da kuma nẽman ya kashe maganar a nan.
( 5 ) Tsẽgumin mãtã a cikin gari da yadda mãtar Azĩz ta yi maganin tsegumin, ta hanyar yiwa mãtan liyafa. Mace bã ta kunyar mãtã 'yan'uwanta ga irin wannan fitina idan ta sãme ta, ita kaɗai, balle mãtã ga sũ duka sun kãmu a cikin tarkon da ya kãma ta. Sai ta gaya musu gaskiyar abin da ya auku a tsakãninta da Yũsufu, a bãyan ta rãma zargin da suka yi mata.