Hausa translation of the meaning Page No 236

Quran in Hausa Language - Page no 236 236

Suratul Yusuf from 5 to 14


5. Ya ce: « Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne. ( 1 ) »
6. « Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima. »
7. Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi ( 2 ) sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa ( 3 ) dõmin mãsu tambaya.
8. A lõkacin da suka ce: ( 4 ) lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.
9. Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai.
10. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: « Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne. »
11. Suka ce: « Yã bãbanmu! ( 5 ) Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi? »
12. « Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne. »
13. Ya ce: « Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi. »
14. Suka ce: « Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra. »
( 1 ) Tarbiyyar uba ga ɗansa.Yaro ƙarami anã rẽnon sa da jawãbi mai laushi a fahimtar matsayin yãron.
( 2 ) Ãyõyi a nan, anã nufin hãlãye waɗanda suka zama darussa na kõyarwa ga mutãne dõmin tarbiyya ga yãra da manya na kõwane matsayi ga rãyuwar ɗan Ãdam.
( 3 ) Yũsufu da ɗan'uwansa shaƙĩƙi, Binyãmĩnu, da saurangõma. Babbansu ga shẽkaru, shi neRaubĩlu, kuma sai Lãwaya. A cikin gidansa aka yi Annabãwa, sai Yahũza kuma shĩ ne shũgabansu a ra'ayi, shĩ ne uban sarãkunansu, sabõda haka sũnansa ya rinjãya a kan ƙabĩlar, aka ce musu Yahũdu.
( 4 ) Hĩrar yãra a tsakãninsu. Sunã tunãnin sõyayyar ubansu gaɗayansu wanda bã ya cikinsu yanzu. Sunã tunãnin yadda zã su sãmi ãdalcin daidaitãwar so daga ubansu bãki ɗayansu. Ɗan'uwansu wanda ubansu yake so, watau Yũsufu, ya sãmi baƙin jini daga gare su dõmin ubansu yana sonsa. Sabõda haka shaiɗan yanã sanya musu tunãnin su yi zunubin rabuwa da shi, sa'an nan su tũba ga Allah.
( 5 ) Sun fara zartar da abin da suka shirya, watau ɗauke Yusufu daga gaban ubansa. Sun fãra da maganar da ubansu yake so game da su tattara da ɗan'uwansu ƙarami. Sunã muhãwara da ubansu sunã nẽman yardarsa don ya bar su su tafi da Yusufu.