Hausa translation of the meaning Page No 248

Quran in Hausa Language - Page no 248 248

Suratul Yusuf from 104 to 111


104. Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu.
105. Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da ƙasa sunã shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sunã bijirẽwa daga gare ta.
106. Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirki.
107. Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa Tãshin Ƙiyãma ta zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba?
108. Ka ce: « Wannan ce hanyãta ( 1 ) ; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba. »
109. Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?
110. Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi.
111. Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.
( 1 ) Bin hukuncin Allah kamar yadda ƙissar Yũsufu ta nũna cẽwa, a ƙõwane hãli mutum ya kasanee akwai yadda Allah Ya yi umurni a wannan hãlin da a bĩ Shi, wanda ya bi umurnin Allah, to, zai ɗaukaka a dũniya kuma Allah bã zai tõzartar da lãdarsa a Lãhira ba.