Hausa translation of the meaning Page No 257

Quran in Hausa Language - Page no 257 257

Suratul Ibrahim from 11 to 18


11. Manzanninsu suka ce musu, « Bã mu zama ba fãce mutãne misã, linku, kuma amma Allah Yanã yin falala a kan wanda Yake so daga bãyinsa, kuma bã ya kasancẽwa a gare mu, mu zo muku da wani dalĩli fãce da iznin Allah. Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara. »
12. « Kuma mẽne ne a gare mu, bã zã mu dõgara ga Allah ba, alhãli kuwa haƙĩƙa Yã shiryar da mu ga hanyõyinmu? Kuma lalle ne munã yin haƙuri a kan abin da kuka cũtar da mu, kuma ga Allah sai mãsu dõgaro su dõgara. »
13. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa Manzanninsu, « Lalle ne munã fitar da ku daga ƙasarmu, kõ kuwa haƙĩƙa, kunã kõmowã acikin addininmu. » Sai Ubangijinsu Ya yi wahayi zuwa gare su, « Lalle ne, Munã halakar da azzãlumai. »
14. Kuma haƙĩƙa, Munã zaunar da ku ga ƙasa a bãyansu. Wancan ne abin gargaɗi ga wanda ya ji tsõron matsayiNa, kuma ya ji tsõron ƙyacẽwãTa.
15. Kuma suka yi addu'ar alfãnu. ( 1 ) Kuma kõwane kangararre mai tsaurin kai ya tãɓe.
16. Daga bãyansa akwai Jahannama, kuma anã shãyar da shi daga wani ruwa, surkin jini.
17. Yanã kwankwaɗarsa, kuma bã ya jin sauƙin haɗiyarsa, kuma mutuwa ta jẽ masa daga kõwane wuri kuma bai zama mai mutuwa ba, kuma daga bãyansa akwai azãba mai kauri.
18. Misãlin waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da tõka wadda iska ta yi tsananin bugãwa da ita a cikin yini mai gũguwa. Ba su iya amfãni daga abin da suka yi tsirfa a kan kõme.Wancan ita ce ɓata mai nĩsa.
( 1 ) Kõwane ɓangare ya yi addu'ar alfãnu ga abin da yake ganin gaskiyarsa. Annabãwa suka yi alfãnu da Allah, kuma mutãnensu suka yi da abin da suke zato alhẽri a gare su.