Hausa translation of the meaning Page No 267

Quran in Hausa Language - Page no 267 267

Suratul Al-Hijr from 91 to 6


91. Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.
92. To, rantsuwa da Ubangijinka! ( 1 ) Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
93. Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
94. Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
95. Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu ( 2 ) izgili.
96. Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.
97. Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã ( na izgili ) .
98. Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
99. Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.
Sũratun Naḥl
Tanã karantar da ni’imõmin da Allah Ya bai wa mutum daga halittarsa, da abincinsa da shiryarwar da Ya yi masa, da hankalin da Ya bã shi, dõmin ya kaɗaita Shi da bautarSa, har zuwa ga ni’imõrnin Lãhira ga wanda ya shiryu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
2. Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi ( 3 ) daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
3. Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
4. Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.
5. Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.
6. Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.
( 1 ) Allah Ya yi rantsuwa da ZãtinSa a kan Shĩ ne Ubangijin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi, dõmin Ya natsar da ransa daga tsõron mãsu yi masa izgili, kuma dõmin Ya ƙarfafa shi ga zartar da aikin da Ya sanya shi na iyar da Manzanci bã da wata fargaba ba.
( 2 ) Mãsu tsananin izgili ga Annabi waɗanda Allah Ya isar masa daga gare su su biyar ne, daga Bani Asad bn Abdul'uzza bn Kusayyi akwai Aswadu bn el Muttalib, Abu zam'ah, kuma daga Bani Zuhrah akwai el Aswad bn Abdu Yagũth. Daga Bani Makhzumi akwai el walid bn Mugira. Daga Bani Sahmi akwai el Ãs bn wã'il. Daga Banĩ Khuzã'a akwai el Harith bn el- Tulãtilah. Su ne mãsu darajar mutãnensu. A lõkacin da suka dõge da sharri, Allah Ya hũtar da Annabi daga sharrinsu da nau'i- nau'i na masĩfu suka halaka. Dubi ƙarin bayãni daga tafsĩrin bn Kathĩr. tsare Annabi daga gare su, tun yanã shi kaɗaia Makka yã isa ya sanya shi ya dõgara ga Allah bãyan abubuwa sun ƙãra yawa da sauƙi.
( 3 ) Saukar da malãiku da Rũhi watau Alƙur'ãni a zãmanin Annabci kõ kuma fahimta da ƙarfin zũciya waɗanda Allah ke sanyãwa ga wanda Ya nufa da jaddada addĩni a kan kõwane ƙarni. Aiko mãsu gargaɗi shĩ ne mafi girman ni'imar Allah a kan mutãne.