Hausa translation of the meaning Page No 274

Quran in Hausa Language - Page no 274 274

Suratul Al-Nahl from 65 to 72


65. Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre.
66. Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima;Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã.
67. Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye ( 1 ) da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.
68. Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi ( 2 ) zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: « Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa. »
69. « Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru. » Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
70. Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi.
71. Kuma Allah Ya fifita sãshenku ( 3 ) a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?
72. Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta?
( 1 ) Yã ambaci abin mãye a cikin abũbuwan ni'ima a gabãnin aharamta giya. Kuma haramtã ta bã ya hanã ta zuma a cikin ni'imõmin Allah ga mutãne dõmin an haramtã ne sabõda tsaron hankalinmu a kan nẽman waɗansu ni'imõmin da suka fĩ ta a Aljanna a inda bã zã a hana ta ba sabõdaƙarẽwar taklĩfi a can. Sabõda haka ne ya ƙãre ãyar da cẽwa: « Akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta. »
( 2 ) Wahayi na ilhama, watau Allah Ya cũsa wa ƙudan zama ilmin yin sã ƙar gidan zuma da gãne hanyõyin tafiya ta kõma gidanta, da cin kõwane irin furen itãce dõmin a fitar dani'imar abin sha mai dãdi ga mutãne, kuma wanda ya ƙunsa dukkan mãgani ga ciwarwatansu. Wannan ni'ima ce babba.
( 3 ) Arziki daga Allah yake, yanãfĩfĩta waɗansu bãyinsa da arziki a kan waɗansu, sa'an nan wanda aka bai wa arziki daga ckinsu bã ya iya mayar da arzikin a tsakãninsa da wani bãwa nasa har su zama daidai a kan arzikin. to, idan haka ne, yaya kuke sanyawaɗansu bãyin Allah daidai da Allah wajen bautarku gare su?