Hausa translation of the meaning Page No 320

Quran in Hausa Language - Page no 320 320

Suratul Ta-Ha from 114 to 125


114. Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa ( 1 ) da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: « Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi. »
115. Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shiba.
116. Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, « Ku yi sujada ga Ãdamu. » Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya.
117. Sai Muka ce: « Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi ( 2 ) ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala. »
118. Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba.
119. « Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba. »
120. Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: « Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa? »
121. Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace.
122. Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar ( da shi ) .
123. Ya ce: « Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala. »
124. « Kuma wanda ya bijire ( 3 ) daga ambatõNa ( Alƙur'ãni ) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar Ƙiyãma yanã makãho. »
125. Ya ce: « Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani? »
( 1 ) Allah Ya umurci Annabi da ya bar gaggãwar karatun Alƙur'ãni a lõkacin da ake yin wahayinsa zuwa gare shi, dõmin kada ya wahala dõmin sũrar tanã karantar da cewa addinin Musulunci sauƙi ne, bai zo dõmin ya wahalar ba. Kuma tsõron yin kuskure yanã sanya yin kuskure mai jãwo wahala kamar yadda Ãdamu ya yi gaggãwar ga tsoron umurnin Allah, sai ya yi mantuwa, ya yi abin da aka hana shi har masifa ta sãmu aka fitar da shi daga Aljanna.
( 2 ) Anã farkar da ɗiyan Ãdamu ga maƙiyin ubansu wanda ya sabbaba musu wahalar zuwa dũniya da haɗuwa da taklĩfi a cikinta. Kuma bin wannan taklĩfi yanã zame masa sauƙi idan sun bĩ shi yadda Allah Ya ce: amma idan sun bi hanyar Shaiɗan, maƙiyinsu, to, bãbu abin da zai sãmu a gare su fãce ƙãrin wahala daga dũniya har Lãhira.
( 3 ) Wanda ya bijire daga ãyõyin Allah, shĩ ne kãfirin da bai yarda da shiga Musulunci ba.