Hausa translation of the meaning Page No 321

Quran in Hausa Language - Page no 321 321

Suratul Ta-Ha from 126 to 135


126. Ya ce: « Kamar wancan ne ãyõyinMu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka. »
127. Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita, ( 1 ) kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa
128. Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda ( kãfirai ) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula.
129. Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta.
130. Sai ka yi haƙuri ( 2 ) a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda.
131. Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i- nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikinsa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa.
132. Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa.
133. Kuma suka ce: « Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa? » Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba?
134. Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: « Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu! »
135. Ka ce: « Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa. »
( 1 ) Wanda ya yawaita, shi ne Musulmi fãsiƙi kõ mai bidi'a yanã ƙara abin da ba a sani ba a cikin addini, ya yawaita shi. Shi ma ya shiga a cikin wahalar dũniya. Kuma ta Lãhira ta fi tsanani.
( 2 ) Haƙuri da riƙe ibãda ta sallõli da tasibĩhi a lõkutanta farilla da na nafila shi ne maganin izgilin mãsu izgili. Tasbĩhi da gõde wa Allah a gabanin fitõwar rãnã ga sallar Asuba, a gabanin ɓacẽwarta ga La'asar, a sã'õ'in dare ga Lisha, da gefukan rãna ga Azahar.