Hausa translation of the meaning Page No 319

Quran in Hausa Language - Page no 319 319

Suratul Ta-Ha from 99 to 113


99. Kamar wancan ne Muke lãbartãwa ( 1 ) a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri ( Alƙur'ãni ) daga gunMu.
100. Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar Ƙiyãma.
101. Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar Ƙiyãma.
102. A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu.
103. Suna ɓõye magana a tsakãninsu, ( Sunã ce wa jũna ) « Ba ku zauna ba ( a cikin dũniya ) fãce kwãna gõma. »
104. Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, « Ba ku zauna ba fãce a yini guda. »
105. Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu ( 2 ) sai ka ce: « Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa, »
106. Sa'an nan Yanã barin ( wurinsu ) faƙo mai santsi.
107. « Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu. »
108. A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya.
109. A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da magan ( 3 )
110. Yanã sanin ( 4 ) abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani.
111. Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye,Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe.
112. Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa.
113. Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa.
( 1 ) Yã kãwo ƙãrin bayãni game da wannan ƙissa a cikin ãyõyin da ke tafe daga nan yadda bin addinin Allah yake da sauƙi a cikin lõkaci gajẽre na dũniya kawai a cikin taƙaitaccen lõkaci, da kuma wuyar bautawa wani ga ɗaukar kãya mãsu nauyi a dũniya da Lãhira, a cikin dõgon lõkaci.
( 2 ) Ana siffanta duwãtsu maɗaukaka da ayyukan dũniya waɗanda bã ibãdar Allah ba, watau al'adu da ibãdõjin da ba ibãdar Allah ba, dukansu kõme yawansu zã su lãlãce a rãnar da Mai kira, wãtau lsrãfĩl, zai bũsa ƙaho na kiran mutãne zuwa ga Tãshin Ƙiyãma, kira wanda bãbu makarkata daga gare shi, watau bã kamar kiran da Annabãwa suka yi ba, wanda waɗansu mutãne suka karkace daga gare shi a nan dũniya.
( 3 ) Bãbu cẽto ga kõwa sai wanda Allah Mai rahama Ya yi masa iznin da yin cẽton, ga wanda aka yi iznin sabõda shi, kuma izni anã yin sa ne da maganar Allah, ba da wata ishãra ba.
( 4 ) Allah Ya san kõme ga halittunsa, su kuwa bã su iya keayewa da sanin kõme game da shi.