Hausa translation of the meaning Page No 329

Quran in Hausa Language - Page no 329 329

Suratul Al-Anbiya from 82 to 90


82. Kuma daga Shaiɗannu ( Mun hõre ) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su.
83. Kuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, ( ya ce: ) « Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama. »
84. Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunãtarwa ( 1 ) ga mãsu ibãda.
85. Kuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri.
86. Kuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sunã daga sãlihai.
87. Kuma mai kifi ( 2 ) a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, « Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai. »
88. Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni.
89. Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, « Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo. »
90. Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata ( 3 ) masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar ( aikata sãɓo ) gare Mu.
( 1 ) Ayyuba Manzon Allah, an jarrabe shi da wahalõlĩ ga jikinsa da halakar ɗiyansa ya yi haƙuri da hukuncin Allah, sai Allah Ya mayar masa da abin da ya halaka, sa'an nankuma ya ƙãrã masa wani kamarsa, dõmin rahamarSa ga mãsu mayar da al'amari a gare shi, da kuma wa'azi ga mãsuibãda dõmin kada aukuwar wata masĩfa ta sanya su kãtsẽwa da rashin ɗaukar haƙuri.
( 2 ) Shĩ ne Yũnus bn Matta. Yãyi hushi da mutãnensa dõmin ba su karɓi addini ba, sai ya bar su tun a gabãnin a yi masa iznin barinsu. Sai Allah Ya jarrabe shi da fãɗãwã cikin ruwa har wani kĩfi ya haɗiye Shi, sa'an nan kuma ya amãyo Shi a bãyan wahala, ya kõma wa mutãnensa. Suka yĩ ĩmãni.
( 3 ) Bãyan mãtarsa ta tsũfa ba ta haihu ba Allah Ya kyautata mahaifarta, ta sãmi cikin Yahaya daga gare shi.