Hausa translation of the meaning Page No 360

Quran in Hausa Language - Page no 360 360

Suratul Al-Furqan from 3 to 11


3. Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa.
4. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: « Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da ( Muhammadu ) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa. » To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.
5. Kuma suka ce: « Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma. »
6. Ka ce: « wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai. »
7. Kuma suka ce: « Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi? »
8. « Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta? » Kuma azzãlumai suka ce: « Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce: »
9. Ka dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin tafarki.
10. Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan ( abu ) : gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje.
11. Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata ( manzanni ) game da Sa'a.