Hausa translation of the meaning Page No 368

Quran in Hausa Language - Page no 368 368

Suratul Al-Shu'ara from 20 to 39


20. Ya ce: « Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi. »
21. « Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni. »
22. « Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla. »
23. Fir'auna ya ce: « Kuma mene ne Ubangijin halittu? »
24. Ya ce: « Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni. »
25. Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, « Bã za ku saurãra ba? »
26. Ya ce: « Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. »
27. Ya ce: « Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne. »
28. Ya ce: « Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta. »
29. Ya ce: « Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru. »
30. Ya ce: « Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa? »
31. Ya ce: « To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya. »
32. Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
33. Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
34. ( Fir'auna ) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, « Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi! »
35. « Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa? »
36. Suka ce: « Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne. »
37. « Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani. »
38. Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
39. Kuma aka ce wa mutãne « Kõ kũ mãsu tãruwã ne?»