Hausa translation of the meaning Page No 378

Quran in Hausa Language - Page no 378 378

Suratul Al-Naml from 14 to 22


14. Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance.
15. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: « Gõdiya ( 1 ) ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai. »
16. Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: « Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar ( Allah ) bayyananna. »
17. Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su ( ga tafiya ) .
18. Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, « Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba. »
19. Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, « Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai. »
20. Kuma ya binciki ( 2 ) tsuntsãye, sai ya ce: « Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne? »
21. « Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne. »
22. Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: « Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce. »
( 1 ) Abin da ke hakkin ni'imar Allah a kan mutum, ya gõde Masa. Dãwũda da Sulaiman Allah Yã bã su ilmi na Annabci sun tsayu da gõdiyarsa a kan aiki da shi, da kuma iƙrãri da cẽwa nĩ'ima ce daga Allah, bã da wani aiki nãsu ba. Annabci da ilmi da sanin maganar tsuntsu da ta aljannu da taturũruwa duka sunã cikin ashĩrin Allah da Yake nũnãwa ta hanyar waɗansu bãyinsa Annabãwa.
( 2 ) Wannan ya nũna tsayuwar sulaimãn da binciken kõme da kõwa a cikin daularsa. Kuma da yadda yake yin tsanani a cikin sauƙi. Wannan ita ce hanyar mulki mai kyau.