Hausa translation of the meaning Page No 377

Quran in Hausa Language - Page no 377 377

Suratul Al-Naml from 1 to 13


Sũratun Naml
Tanã karantar da cẽwa Allah Yanã da asirrai, bã su da iyãka,Yanã nũna sãshensu ta hannun waɗansu mutãne bãyinsa da a cikin littattafanSa, dõmin mũminai su ƙãra ƙarfin ĩmãni, kuma su yi aiki da Sharĩ’a da Ya aza su a kanta.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ɗ.S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa.
2. Shiriya ce da bushãra ga mũminai.
3. Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ,sunã yin yaƙĩni.
4. Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa.
5. Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba ( a dũniya ) , kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra.
6. Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa ( 1 ) ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani.
7. A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa « Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi. »
8. To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, « An tsarkake wanda yake cikin ( wurin ) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu. »
9. « Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima. »
10. « Kuma ka jẽfa sandarka. » To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, « Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa. »
11. « Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. »
12. « Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai. »
13. To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.
( 1 ) Lãhira da ĩmãni da ita sunã a cikin ashĩran Allah. Haka karɓar Alƙur'ãni daga Allah yanã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana a Littafi. Ganin Mũsa ga wutã da abubuwan da suka auku a wurin game da maganar Allah a gare shi da jũyãwar sanda macijiya da kõmawarta sanda da jũyãwar hannunsa fari ƙal da jũyãwarsa zuwa ga asalinsa, duka sunã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana su ga wani mutum.