Hausa translation of the meaning Page No 392

Quran in Hausa Language - Page no 392 392

Suratul Al-Qasas from 51 to 59


51. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar ( 1 ) da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni.
52. Waɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa ( Alƙur'ãni ) , su mãsu ĩmãni ne da shi. ( 2 )
53. Kuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: « Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa. »
54. Waɗancan anã ba su lãdarsu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa.
55. Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, « Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai ( da husũma ) . » ( 3 )
56. Lalle ne kai bã ka shiryar ( 4 ) da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.
57. Kuma suka ce: « Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu ( 5 ) daga ƙasamiu. » Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
58. Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda.
59. Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci.
( 1 ) Attaura da Alƙur'ãni. Ayyukan Annabawa sãshenSu sun sãdu da sãshe.
( 2 ) Mun sãdar da ilmin Taurãtada ilmin Alƙur'ãni, kowãne ya gaskata wani, ko kuwa Mun sãdar da maganar Alƙur'ani, wata ta bi wata, babu bambanci ga fasãha da abũbuwan ban mãmaki a cikinsu.
( 3 ) Waɗanda aka bai wa littafi a gabãnĩn Alƙur'ãni, sũ ne Yahũdu da Nasãra,waɗansu daga cikin Malamansu sun musulunta, kamar Abdullahi bn salãmi daga Yahũdu, da Nasãran Najrãna daga Nasãra, sun musulunta. Idan ba'ali ya musulunta sai a ce dukansu ke nan sun musulunta, sai wanda ya yi girman kai ya ƙigaskiya. Bã zã a kula da shi ba.
( 4 ) Annabi, tsĩra da aminei su tabbata a gare shi, ya kasance yanã son mutãnensa Ƙuraishãwa su shiryu har dai Amminsa Abu Talib, sai Allah Ya gaya masa cẽwa shiriya ga hannunsa take, shi kaɗai, kuma sai wanda Ya so, shi ne zai shiryu, amma kuma akwai daga cikin dalĩlai bayyanannu maganar hijira kamar yadda ãyar da ke tafe ta bayyana.
( 5 ) Wanda ya makkana musu Hurumi ya zama amintacce, yanã iya tsare bãwanSa kuma Yabã shi arziki a kõ'ina yake a cikin ƙasa, sabõda haka tsõron fita daga Hurumi da tsõron wuyar abinci a wurin baƙunci, bã zai hana mũmini ya yihijira da addininsa ba zuwa wurin yardar Allah.