Hausa translation of the meaning Page No 396

Quran in Hausa Language - Page no 396 396

Suratul Al-Qasas from 85 to 6


85. Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: « Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananna. »
86. Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako ( 1 ) ga kãfirai.
87. Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka.
88. Kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskarSa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. ( 2 )
Sũratul ‘Ankabũt
Tanã karantar da cẽwa Kalmar ĩmãni kawai bã ta isa sai da aikata abin da ta ƙunsa. Kuma Allah na jarraba Musulmi dõmin a fitar da munafukai daga cikin nagari.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. M̃.
2. Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: « Mun yi ĩmãni, » alhãli kuwa bã zã a fitine su ba? « »
3. Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.
4. Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana.
5. Wanda ya kasance yanã fãtan gamuwa da Al1ah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma ( Allah ) Shĩ ne Mai ji, Masani.
6. Kuma wanda ya yi jihãdi, to, yanã yin jihãdin ne dõmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tãlikai.
( 1 ) Taimakon, shi ne ka yi bũrin musuluntarsu har ka wahala dõmin a sauƙaƙe ma hukuncin hijira wadda Allah Ya yi umurni da a yi ta a bãyan musulunta sai ka iyar da Manzanci, shiryarwa kuwa ga hannun Allah take. Wannan ãyã tanãnunãwa bayyana ƙaryar mãsu da'awar cẽwa wani mutum yanã bai wa wani ĩmãni ko ya karɓe shi daga gare shi. Kõwa a cikin tsõro yake, sai wanda Allah Ya sanya shi cikin aminci. Allah Ya sanya mu cikin amincinSa dõmin rahamarsa.
( 2 ) Wannan ãyã ta ƙarshen sũrar, ta tãra ilmin da sũrar ta karantar a cikin abũbuwa biyar da ta zãna.