Hausa translation of the meaning Page No 5

Quran in Hausa Language - Page no 5 5

Suratul Al-Baqarah from 25 to 29


25. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, ( 1 ) sai su ce: « Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka, » Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne.
26. Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: « Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ( 2 ) ya zama misãli? » na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.
27. Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
28. Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?
29. Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita ( 3 ) zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne.
( 1 ) Gõnaki kõ gidãjen Aljanna.
( 2 ) Misãli kamar mãtan Aljannamãsu tsarki. Ba mãtã ba kõ da sauro ko abin da ya fi, kõya kãsa sauro, to, akwai hikima a cikin halittarsa, wadda zã ta jãwo hankalin mai hankali ga ĩmãni da Allah sabõda ita.
( 3 ) Ya daidaita, watau Ya yi nufi; « Sa'an nan » yana amfãnar da jeranta aiki bã jerantar nufi ba, dõmin sifõfn Allah dukansu, bã fãrarru ba ne.