Hausa translation of the meaning Page No 403

Quran in Hausa Language - Page no 403 403

Suratul Al-Ankabut from 53 to 63


53. Kuma suna nẽman ka da gaggauta azãba, to, bã dõmin ajali ƙayyadadde ba, dã azãba ta jẽ musu kuma lalle dã tanã iske su bisa ia abke, alhãli kuwa sũ ba su sani ba.
54. Sunã nẽman ka da gaggauta azãba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce gakãfirai.
55. Rãnar da azãba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya ( 1 ) ce: « Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
56. Yã bãyiNa, waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle fa ƙasãTa mai yalwã ( 2 ) ce, sabãda haka ku bauta Mini.
57. Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku.
58. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zã Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidãjen bẽne, ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon mãsu aikin ƙwarai.
59. Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu kawai.
60. Kuma da yawa ( 3 ) dabba wadda bã ta ɗaukar abincinta Allah Yanã ciyar da ita tãre da ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi.
61. Lalle idan ka tambaye su: « Wãne ne ya halitta sammai da ƙasã kuma ya hõre rãnã da watã? » Lalle sunã cẽwa Allah ne. TO, yãya ake karkatar da su ( 4 ) ?
62. A1lah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin bãyinsa kuma Yanã ƙuntãtãwa ga ( wanda, Yake so ) . Lalle Allah, Masani ne ga dukan kõme.
63. Kuma lalle idan ka tambaye su. « Wãne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta? » Lalle sunã cẽwa, « Allah ne. » Ka ce: « Gõdiya tã tabbata ga Allah. » Ã'a, mafi yawansu bã su hankalta.
( 1 ) Ga wata ruwãyar « Mu » matsayin « Ya » watau Malã'iki waki1in azãbarsu.
( 2 ) Tun da ƙasa nã da yalwã, sai mutum ya yi hijira zuwa wurin da yake mai sauƙi a gareshi, ya bauta wa Allah da sauƙi, idan garinsu ya buwãye shi.
( 3 ) Sabõda haka tunãnin abinci kada ya hana ku yin hijira zuwa wurin yardar Allah, Mai ciyar da dabbõbin da bã su tattalin abincinsu.
( 4 ) Yãya ake karkatar da su daga hijira dõmin tsõron yankẽwar abinci, alhãli kuwa sun tafi wurin yardar wanda Ya halitta sammai da ƙasã? Yin hijira yanã a cikin jarrabãwar Allah ga Musulmi.