Hausa translation of the meaning Page No 404

Quran in Hausa Language - Page no 404 404

Suratul Al-Ankabut from 64 to 5


64. Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani.
65. To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki.
66. Dõmin su kãfirce wa abin da Muka bã su kuma dõmin su ji dãɗi sa'an nan kuma zã su sani.
67. Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka kãfirta?
68. Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai?
69. Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa ( ga addĩninsu ) .
Sũratur Rũm
Tanã karantar da cẽwa duka abũbuwan dũniya sunã da dangantaka da junansu, dangantaka bayyananna kõ ɓõyayya. Kuma zumuntarsu na gudãna gwargwadon dangantakarsu da jũna ga jiki da ma’ana.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. M̃.
2. An rinjãyi Rũmawa. ( 1 )
3. A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya.
4. A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki.
5. Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
( 1 ) Rũmãwa Kiristoci ne mãsu aiki da littãfi, sunã faɗa da Fãrisãwa mãsu bautã wa wutã. Fãrisa suka rinjãyi Rumãwa, sabõda haka Ƙuraishãwa suka ji dãɗi sabõda alfãnu cẽwa zã su rinjãyi Musulmi idan sun yi faɗa. A bãyan saukar surar, sai Musulmi suka yi farin ciki sabõda alfãnu cẽwa sũ kuma zã su rinjãyi Ƙuraishãwa. Wannan ya sanya Abũbakar ya yi ƙuri'a da Ubaiyu bn Halafa kan rãƙuma gõma a cikin shẽkaru uku. Sai Annabi ya ce wa Abũbakar ya ƙãra rãkuma da ajãli zuwa shẽkaru tara. A bãyan shekaru bakwai sai Rũmawa suka ci nasara a kan Fãrisãwa, kuma wannan ya yi daidai da Badar,watau rãnar da Musulmi suka ci nasara a kan Ƙuraishãwa. Abũbakar ya ci rãƙumansa daga magãdan Ubaiyu. Amma sai ya yi sadaka da su da umurnin Annabi, dõmin Allah Yãhana Musulmi su yi cãca a lõkacin.