Hausa translation of the meaning Page No 415

Quran in Hausa Language - Page no 415 415

Suratul Al-Sajdah from 1 to 11


Sũratus Sajda
Tanã karantar da wa’azi da Alƙur’ãni gaskiya ne, mabiyinsa shĩ ne mai rĩba, wanda ya sãɓã masa, shĩ ne mai hasãra.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. M̃.
2. Saukar da Littafin bãbu shakka a gare shi, daga Ubangijin tãlikai yake.
3. Kõ sunã cẽwa ( Muhammadu ne ) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu.
4. Allah ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba?
5. Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa.
6. Wannan shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwãyi, Mai jinƙai.
7. Wanda Ya kyautata kõme, Wanda Ya halitta shi. Shi ne kuma Ya fãra halittar mutum daga lãka.
8. Sa'an nan Ya sanya ɗiyansa daga wani asali na wani ruwa wulãkantacce.
9. Sa'an nan Ya daidaita shi, kuma Ya hũra a cikinsa, daga ruhinSa kuma Ya sanya muku ji, da ganunuwa da zukãta. Gõdiyarku kaɗan ce ƙwarai.
10. Kuma suka ce: « Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã zama a cikin wata halitta sãbuwa? » Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai
11. Ka ce: « Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku. ( 1 ) Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku. »
( 1 ) Watau bã ku ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, sabõda haka tãyarwar ma bãkũ zã ku yi ta da kanku ba,balle ku yi musu.