Hausa translation of the meaning Page No 433

Quran in Hausa Language - Page no 433 433

Suratul Saba from 40 to 48


40. Kuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, « Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa? »
41. Sukace: « Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bã su ba. Ã'a,sun kasance sunã bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani. »
42. Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda « kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa. »
43. Kuma idan an karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, sai su ce: « Wannan bai zama ba fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã bauta wa. » Kuma su ce: « Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga. » Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: « Wannan bã kõme ba fãce sihiri ne bayyananne. »
44. Kuma ba Mu bã su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karãtun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabãninka!
45. Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata ,alhãli kuwa ba su kai ushurin- ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata ManzanniNa! To, yãya musũNa ( ga maƙaryata ) ya kasance?
46. Ka ce: « Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani. »
47. Ka ce: « Abin da na rõƙe ku na wani sakamako, to, amfãninsa nãku ne. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma shi Mahalarci ne a kan dukan kõme. »
48. Ka ce: « Lalle Ubangijina Yanã jẽfa gaskiya. ( Shi ) Masanin abũbuwan fake ne. »