Hausa translation of the meaning Page No 434

Quran in Hausa Language - Page no 434 434

Suratul Saba from 49 to 3


49. Ka ce: « Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bã ta iya fara ( kome ) kuma bã ta iya mayarwa. »
50. Ka ce: « Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci. »
51. Kuma dã kã gani, a lõkacin da suka firgita, to, bãbu kuɓuta, kuma aka kãma su daga wuri makusanci.
52. Kuma suka ce: « Mun yi ĩmãni da Shi. » To inã zã su sãmu kãmãwa daga wuri mai nisa?
53. Kuma lalle sun kãfirta da Shi a gabãnin haka, kuma sunã jĩfa da jãhilci daga wuri mai nĩsa.
54. Kuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kõkanto.
Sũratu Fãɗir
Tanã karantar da cẽwa bauta wa Allah shi ne mabuɗin dukan alhẽri kuma bautar nan da sanin yadda ake yin ta daga gare Shi yake.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Gõdiya ta tabbata ga Allah, Mai fãra halittar sammai da ƙasã, Mai sanya malã'iku manzanni mãsu fukãfukai, bibbiyu, da uku- uku da hurhuɗu. Yanã ƙãrãwar abin da Ya ke so a cikin halittar. Lalle Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
2. Abin da Allah Ya buɗa wa mutãne daga rahama, to, bãbu mai riƙewa a gare shi, kuma abin da Ya riƙe, to, bãbu mai saki a gare shi, waninSa, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
3. Yã kũ mutãne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasã? Bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?