Hausa translation of the meaning Page No 441

Quran in Hausa Language - Page no 441 441

Suratul Ya-Sin from 13 to 27


13. Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni ( 1 ) suka jẽ mata.
14. A lõkacin da Muka aika ( Manzannin ) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa ( su ) da na uku, sai suka ce: « Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku. »
15. Suka ce: « Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi. »
16. Suka ce: « Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku. »
17. « Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne. »
18. Suka ce: « Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku. »
19. Suka ce: « Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi. »
20. Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: « Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan. »
21. « Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne. »
22. « Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku? »
23. « Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã. »
24. « Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna. »
25. « Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni. »
26. Aka ce ( 2 ) ( masa ) , « Ka shiga Aljanna. » Ya ce, « Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani. »
27. « Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama. »
( 1 ) Su Manzannin Ĩsã ne zuwa Antãkiya, bãbban garin kasar Rũmu. Sũ ne Yõhana da Pulis. Na uku, shĩ ne sham'ũn. Mutumin da ya jẽ yanã gaggawa, shi ne Habĩb Masassaki wanda ya fãra gamuwa da Manzannin farko, ya yi ĩmãni da su, sa'an ya jẽ yanã wa'azi ga mutãnensa.
( 2 ) An ce masa haka a bayan mutãne sun kashe shi sabõda ĩmãninsa. Wannan shi ne sakamakon mai wa'azi idan ya yi shahada a kan aikinsa na wa'azi.