Hausa translation of the meaning Page No 442

Quran in Hausa Language - Page no 442 442

Suratul Ya-Sin from 28 to 40


28. Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama ( 1 ) a kan ( halaka ) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba.
29. Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu.
30. Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili.
31. Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da ( mutãnen ) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba?
32. Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu.
33. Kuma ãyã ce a gare su: Ƙasã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci.
34. Kuma Muka sanya, a cikinta ( ƙasã ) , waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta.
35. Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba?
36. Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba.
37. Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu.
38. Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.
39. Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa.
40. Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo.
( 1 ) Wãtau halakar da su abu nemai sauƙi a gare Mu, ba Mu yi bukãtar saukar da wasa sõjõjin malã'iku daga samã ba.