Hausa translation of the meaning Page No 455

Quran in Hausa Language - Page no 455 455

Suratul Sad from 27 to 42


27. Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã.
28. Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata?
29. ( Wannan ) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.
30. Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi ( Sulaimãn ) mai mayar da al'amari ne ga Allah.
31. A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, ( 1 ) a lõkacin maraice.
32. Sai ya ce: « Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har ( rãnã ) ta faku da shãmaki! »
33. « Ku mayar da su a gare ni. » Sai ya shiga yankansu ( 2 ) da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.
34. Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini ( 3 ) Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
35. Ya ce: « Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna. ( 4 ) Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta. »
36. Sabõda haka Muka hõre masa iska ( 5 ) tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa.
37. Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa ( a cikin kõguna. )
38. Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa.
39. Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike.
40. Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma.
41. Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba ( 6 ) a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: « Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba. »
42. Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.
( 1 ) Shĩ ne dõki mai tsayuwa a kan ƙafãfu uku. Wannan yanã nũna asalinsa mai kyau ne.
( 2 ) Sulaimãna ya yanka dawãkin,dõmin kallonsu yã hana shi salla, wadda take farlu ainin ce a gare shi, amma tattalin kãyan yãƙi farlu kifãya ce. Anãgabãtar da farlu ainin a kan farlu kifãya. Wannan kuma ya nũna cẽwa anã cin dõki idan wani dalĩli bai hana ba. Dũbi Sũra ta 16, ãyã ta 8.
( 3 ) Wata rãna Sulaiman ya yi tunãnin ya sãdu da mãtansa ɗari uku, dõmin su yi cikunna su haifi diya mãsu taimakonsa jihãdi fi sabilillahi, amma ya manta, bai ce in Allah Yã so ba. Sai ya sãdu da su, ba su yi cikin ba, sai guda ɗaya daga cikinsu, kuma ta haife shi bãbu rai. Ma'anar kissar, ita ce ko aikin Allah, sai mutum ya mayar da yinsa ga mashĩ'ar Allah, sa'an nan zai ci nasara a kansa.
( 4 ) Yã yi wannan addu'a dõminkada wani ya yi alfahari da sarauta a bãyansa, ya halaka kuma ya halakar da wani. Sarauta ita ce asalin girman kai da alfahari. Bã ka ganin wanda ya shiga wa sarki, dõmin ya gaishe shi, idan ya fito daga gare shi, sai ya ɗõra yin tãƙama dõmin abin da zuciyarsa ta ɗẽbo daga girman kan sarkin da alfaharinsa?
( 5 ) An hore masa iska matsayin dawãkin da ya yanke dõmin Allah. An hõre masa aljannu dõmin niyyarsa ta sãmun diya mãsu jihãdi dõmin Allah.
( 6 ) Wannan ƙissa tanã nũna haƙuri ga riƙon iyãli, mulkin ƙasã da mulkin gida duka daidai suke, sai yadda Allah Ya yi umurni a yĩ su. Haka mallakar rai idan mutum bai bi umurnin Allah ba a cikinsu, sai su buwãye shi tsarẽwa, kamar yadda mulkin ƙasa ke buwãya a riƙe shi tãre da kãfirci da zãlunci.