Hausa translation of the meaning Page No 454

Quran in Hausa Language - Page no 454 454

Suratul Sad from 17 to 26


17. Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa ( na izgili ) , kuma ka ambaci bãwanMu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne.
18. Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã.
19. Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi.
20. Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima ( 1 ) da rarrabẽwar magana.
21. Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci?
22. A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: « Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya. »
23. « Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana. »
24. ( Dãwũda ) ya ce: « Lalle, haƙiƙa ya zãlunce ( 2 ) ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. » Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara,kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
25. Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurinMu, da kyaun makõma.
26. Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi
( 1 ) Hikima, ita ce Annabci, rarrabe magana, shĩ ne sanin hanyar yin sharĩ'a da rarrabe mai ƙãra daga wanda aka yi ƙãra, da nẽman shaidu daga mai ƙãra da nẽman rantsuwa ga mai musu.
( 2 ) Dãwũda ya yi hukunci da zãlunci ga wanda ya yi ƙãra, sabõda abin da ya rufe shi na ƙin zãluntar mai rauni wanda Allah Ya hana. Nauyin wani laifi ya rufe shi daga tunãwa da wani laifi, watau yin hukunci tun binciken shari'a bai cika ba, sabõda iya maganar wani abõkin ƙãra. Wannan shĩ ne fitinar da ta same shi kawaikuma a kanta ya yi nadãma, kuma a kanta ne Allah Ya yi masa gargaɗin kada ya bi son rai mai sanya hushi kõ yarda ga abin da bai cancanci haka ba. Yarda da wata ƙissar mãtar Uriya wadda Yahũdãwa ke sanyãwa, a nan, kãfirci ne ga Musulmi, dõmin ta kõre ismar Annabãwa, kuma ba ta dãce da lafazin Alƙur'ãni ba.