Hausa translation of the meaning Page No 458

Quran in Hausa Language - Page no 458 458

Suratul Sad from 84 to 5


84. ( Allah ) Ya ce, « To, ( wannan magana ita ce ) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa. »
85. « Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya »
86. Ka ce: « Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa. »
87. « Shĩ ( Alkur'ãn ) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta. »
88. « Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa ( 1 ) a bayan ɗan lõkaci. »
Sũratuz Zumar
Tanã karantar da cewa sanin akwai Allah, da sanin Shĩ ne Ya halitta kõme, ba ya isa ga ĩmãni, sai an tsarkake ibada gare Shi.Wãtau tauhĩdin Rubũbiyya, bã ya isa sai da na Ulũhiyya.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima.
2. Lalle Mũ Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka, da gaskiya. Sabõda haka, ka bauta wa Allah kanã mai tsarkake addini a gare Shi.
3. To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ( 2 ) ba, ( sunã cẽwa ) « Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja. » Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci.
4. Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
5. Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara.
( 1 ) Watau za ku san aikin da Alƙur'ãni zai yi wa waɗanda suka yi aiki da shi a bãyanɗan lõkaci, sã'ilin da zã su ɗaukaka a idan dũniya' su zama wadãtattu a bãyan talauci, kuma sarãkuna a bãyan mõranci. Wannan kuwa ya auku inda suka mallake dũniya a cikin rabin ƙarni.
( 2 ) Bauta wa gumãka da hidimarshehunai da suka mutu waɗanda suka shirya wani sãbon abu da bãbu ga sunnar Annabi duka ɗaya suke, dõmin kõwanensu kiran wanin Allah sabõda nẽman ãgaji ne.