Hausa translation of the meaning Page No 457

Quran in Hausa Language - Page no 457 457

Suratul Sad from 62 to 83


62. Kuma suka ce: « Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai? »
63. « Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne? »
64. Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã.
65. Ka ce: « Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa. »
66. « Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara. »
67. Ka ce: « Shĩ ( Alkur'ãni ) babban lãbãri ne mai girma » .
68. « Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi! »
69. « Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a ( malã'iku ) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma. »
70. « Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa. »
71. A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, « Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã. »
72. « Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra ( wani abu ) daga RuhĩNa a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi. »
73. Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya.
74. Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
75. ( Allah ) Ya ce, « Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne? »
76. Ya ce, « Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã. »
77. Ya ce, « To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne. »
78. « Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako. »
79. Ya ce, « Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su. »
80. Ya ce, « To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri, »
81. « Zuwa ga yinin lõkaci sananne. »
82. Ya ce, « To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya. »
83. « Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su. »