Hausa translation of the meaning Page No 484

Quran in Hausa Language - Page no 484 484

Suratul Al-Shura from 11 to 15


11. ( Shĩ ne ) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma ( Ya sanya ) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.
12. Shĩ ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yanã shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yanã hukuntãwa. Lalle ne, Shĩ Masani ne ga dukan kõme.
13. Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. ( 1 ) Abin da kuke kira zuwa gare shi, ( 2 ) ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa.
14. Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma ( 3 ) tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.
15. Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, « Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take. »
( 1 ) Ku bi umurnin Allah kamar yadda Ya aza muku hukunce- hukuncenSa, kada ku karkace da bin umurnin waɗansu na dabam waɗanda bã Allah ba, kõ kuma kada ku bi son zũciyarku. Bin umurnin wani zai sanya ku sãɓã wa jũnanku, ku rarrabu, ku rasa ƙarfi a kan maƙiyanku. Wanda ya bi umurnin waɗansu, waɗanda bã Allah ba, to, ya yi shirki da Allah ke nan kuma haɗuwar mãsu bin umurnin waɗansu waɗanda bã Allah ba, to, tanã da wuya. Wannan ãya ta hana bin ɗarĩƙõƙin ƙungiyõyin sũfãye duka, dõmin bin su, bin umurnin waɗansu ne waɗanda bã Allah ba kuma yanã rarraba Musulmi, su zama ƙungiya- ƙungiya, da sãɓãni mai nĩsa. Bã zã a ce ba, « Ã'aha! Wannan ãya ta sauka ga Yahũdu da Nasãra kawai » dõmin ãyõyi biyu l4 da l5, mãsu bin wannan, sun gama harda Musulmi, dõmin umurni ga Annabi, umurni ne sabõda al'ummarsa. Kuma sãɓãnin mãsu ɗariƙõƙi sãɓãni ne a kan asali watau aƙida, bã sãɓãnine a kan rassuna na furũ'a ba. Sabõda haka bãbu ƙiyayya a tsakãnin mabiya mazhabõbi, dõmin sãɓãninsu, na fahimta ne kawai. Sãɓãni ga rĩshe, rahama ce, amma sãɓãni ga asali azãba ce.
( 2 ) Watau haɗuwar jama'aga bin addini guda, bã da sãɓawa ba ga asalinsa. Wanda ya ce: An saukar wa wani mutum, baicin Muhammadu, da wani abu daga Allah, to, shĩ ya sãɓã wa asali. Sãɓãwa ga asali kãfirci ne.
( 3 ) Kalmar da ta gabãta, ita ce « Allah bã zai halaka mutane ba sabõda zunubi sai ajalinsu ya zo. » Zãlunci da ke hana su haɗuwa a bãyan sanin gaskiya, shi ne hassadar jũna, sa kwaɗayi da son shugabanci a cikin mu'amala.