Hausa translation of the meaning Page No 483

Quran in Hausa Language - Page no 483 483

Suratul Al-Shura from 1 to 10


Sũratush Shũrã
Tanã karantar da muhimmancin haɗuwar jama’ar Musulmi da hanãwar rarrabar kalmarsu, a kõwane hãli.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ḥ. M̃.
2. Ĩ. Ṣ̃.
3. Kamar wancãn ( 1 ) ( asĩrin ) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka .
4. ( Allah ) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
5. Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
6. Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba.
7. Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa ( Alƙur'ãni ) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu ( Makka ) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr.
8. Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãluMai bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki.
9. Kõ kuma sun riƙi waninSa majiɓinta? To Allah Shĩ ne Majiɓinci, kuma Shĩ ne ke rãyar da matattu alhãli kuwa Shĩ, Maiĩkon yi ne a kan dukan kõme.
10. Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa ( a mayar da shi ) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna.
( 1 ) Asirin haɗa jama'a bã zã su rarrabu ba. Watau su riƙi Allah Shi kaɗai ne Ubangiji Mai yin umurni ko hani, kuma su riƙi cẽwa Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi, shĩ ne cikamakin Annabãwa, bãyansa bã a bai wa kõwa kõme fãce fahimta ga abin da ya zo da shi.