Hausa translation of the meaning Page No 488

Quran in Hausa Language - Page no 488 488

Suratul Al-Shura from 45 to 51


45. Kuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, « Lalle ne, mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar Ƙiyãma. » To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya.
46. Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra.
47. Ku karɓã wa Ubangijinku tun gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare shi daga Allah, bã ku da wata mafaka a rãnar nan, kuma bã ku iya yin wani musu.
48. To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne.
49. Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda Yake so.
50. Kõ kuma Ya haɗa su maza da mãtã, kuma Yanã sanya wanda Ya so bakarãre. ( 1 ) Lalle shi, Mai ilmi ne, Mai ĩkon yi.
51. Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana ( 2 ) fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.
( 1 ) Bakarãre, shi ne wanda bã ya haihuwa.
( 2 ) Annabãwa a lõkacin da AllahYa yi musu magana ba su gan shi ba, sai dai su ji maganarsa kamar yadda Musã ya ji, kõ kuma da wãsiɗar malã'ika kamar sauran Annabãwa, kõ kuwa da ilhami watau ya san hukunci ba da magana kõ wani wãsiɗar malã'ika ba. Ilhãmin Annabãwa da mafarkinsu gaskiya ne. Ilhãmi da mafarkin sauran mutãne bã ya zuma hujja sai idan yã dãce da shari'a, sai a yi aiki da shi a kan shari'a bã a kan mafarkin ko ilhãmin ba.