Surah Az-Zukhruf | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 492
Suratul Zukhruf from 34 to 47
34. Kuma a gidãjensu, Mu sanya ) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa.
35. Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce.
36. Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa.
37. Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne.
38. Har a lõkacin da ( abõkin Shaiɗan ) ya zo Mana ( ya mutu ) sai ya ce: ( wa Shaiɗan ) « Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum! »
39. Kuma ( wannan magana ) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba.
40. Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?
41. To, kõ dai Mu tafi ( 1 ) da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu.
42. Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne.
43. Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciyl.
44. Kuma shi ( abin wahayin ) ambato ( na ɗaukaka ) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku.
45. Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, « Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun ( Allah ) , Mai rahama, anã bauta musu? »
46. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: « Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu. »
47. To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyinMu, sai gã su sunã yi musu dãriya.
( 1 ) Mu tafi da kai, watau Mu karɓi ranka, ka mutu, to, dã Mun yi musu azãba ke nan, dõmin sun rasa mai shiryar da su.