Hausa translation of the meaning Page No 501

Quran in Hausa Language - Page no 501 501

Suratul Al-Jathiya from 23 to 32


23. Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi, ( 1 ) Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?
24. Kuma suka ce: « Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa ( da haihuwa ) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani. » Alhãli kuwa ( ko da suke faɗar maganar ) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.
25. Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: « Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya. »
26. Ka ce: « Allah ne ke rãyar ( 2 ) da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar Ƙiyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. »
27. « Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã ( ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa ) zã su yi hasãra. »
28. Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. ( A ce musu ) « A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
29. « Wannan littãfinMu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasanceMuna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa. »
30. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne.
31. Kuma amma waɗanda suka kãfirtã ( Allah zai ce musu ) : « Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi? »
32. « Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto ( game da ita ) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba. » '
( 1 ) Ilmin Allah bã ya da iyãka, Yanã bũɗa shi ga wanda Ya ga dãma, a inda kõ a lõkacin da Ya ga dãma, amma dai duk ilmin da bai saukar da shi ga Annabi Muhammadu ba, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, to, bã a aiki da shi ga hukunci kõ sharĩ'a, wanda ya bi shi kuwa, to, ya ɓace ga aikinsa, bã ya cikin shiryayyu mãsu zaman lãfiya a dũniya kuma su shigĩ a Aljanna a Lãhira, dõmin sharaɗin haka shĩh ne binsunna. Wanda ya bar sunna kuwa, ya yi kuskuren hanya, bãbu mai shiryar da shi kuma sai Allah idan Yã so shi da rahama, watau Ya sanya shi ya tũba. Wannan ya nũna cẽwa ibãda da mu'ãmala duka ɗaya suke ga Musulunci, barin aiki da sharĩ'a a cikin kõwannensu duka, kãfirci ne ga wanda ya halatta yin haka nan. Mafi yawan kãfircin da ya sãmi Musulmi, ya zo musu ne ta hanyar barin mu'ãmalõli da sharĩ'ar Allah, suka &# 82auki yin salla da mai kama da ita, shi kaɗai neMusulunci, suka kãfirta da haka.
( 2 ) Wãtau ba kũ ne ke rãyuwa da kanku ba, sai an rãyar da ku, haka ne ga mutuwa, bã ku ne ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, kuma Allah Shi Ɗaya ke iya rãyarwa ko matarwa. To, yãya ne zã ku ƙi bin sharĩ'ar da Ya umurce ku da binta?