Hausa translation of the meaning Page No 500

Quran in Hausa Language - Page no 500 500

Suratul Al-Jathiya from 14 to 22


14. Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, ( 1 ) dõmin ( Allah ) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
15. Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.
16. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai ( 2 ) ( wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya ( a zãmaninsu ) .
17. Kuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa ( jũna ) .
18. Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin.Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba.
19. Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.
20. wannan ( Alkur'ãni ) hukunce- hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni.
21. Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!
22. Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba.
( 1 ) Kwanukan Allah, sũ ne masĩfu waɗanda ke sãmun kãfirai waɗanda bã su bin sharĩ'ar Allah. Wãtau Allah Yaumurci Annabi ya gaya wa Musulmi, cẽwa wanda bã ya tsõron masĩfu sabõda ya ki aiwatar da sharĩ'ar Allah a kansa to kada Musulmi su dãmuda shi, watau kãfiran amãna nã iya bin dõkõkinsu na al'ãda, bãbu ruwan Musulmi matuƙar dai ba su shũka wata fitina ba a gare su. A bãyan haka Allah zai sãka wa kõwa game da aikinsa.
( 2 ) Bã Musulmi kawai aka aikowa Manzo ba ba, su kawai aka bã su sharĩ'a ba kuma aka umurce su da binta ba, Banĩ Isrã'ĩla ma an bã su haka kuma sunɗaukaka a kan mutãne a lõkacin da suka yi aiki da sharĩ'ar, kuma suka ƙasƙanta a lõkacin da suka bar aiki da ita. Musulmi ma haka suke idan sun bar sharĩ'ar da Allah Ya aza su a kanta, zã su ƙasƙanta yadda Yahũdawa suka ƙasƙanta.