Hausa translation of the meaning Page No 530

Quran in Hausa Language - Page no 530 530

Suratul Al-Qamar from 28 to 49


28. Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu ( da rãƙumar ) , kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.
29. Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,
30. To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
31. Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
32. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
33. Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
34. Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.
35. Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
36. Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
37. Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. « To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa. »
38. Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
39. To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
40. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur,ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
41. Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.
42. Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
43. Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?
44. Kõ zã su ce: « Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara? »
45. Zã a karya ( 1 ) tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
46. Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
47. Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
48. Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. « Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar. »
49. Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
( 1 ) Bushãra ce ga Annabi, cẽwa zai yi yãƙi da Kuraishi kuma zai rinjãye su. Sa'an nan yãkin ya auku a Badar.