Hausa translation of the meaning Page No 529

Quran in Hausa Language - Page no 529 529

Suratul Al-Qamar from 7 to 27


7. Ƙasƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
8. Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, « Wannan yini ne mai wuya! »
9. Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: « Shi mahaukaci ne. » Kuma aka tsãwace shi.
10. Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa ( ya ce ) , « Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako. »
11. Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
12. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
13. Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan ( jirgi ) na alluna da ƙũsõshi.
14. Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
15. Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
16. To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
17. Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
18. Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
19. Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.
20. Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
21. To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
22. Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
23. Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
24. Sai suka ce: « Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã. »
25. « Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai! »
26. Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
27. Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ( 1 ) ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
( 1 ) Mutãnen Sãleh sun nẽmi mu'ujiza da rãƙuma, a fitar da ita daga dũtse, sai aka fitar da ita, kuma aka raba ruwan sha a tsakãninsu da ita.