Hausa translation of the meaning Page No 532

Quran in Hausa Language - Page no 532 532

Suratul Al-Rahman from 17 to 40


17. Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
18. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
19. Yã garwaya tẽku biyu ( ruwan dãɗi da na zartsi ) sunã haɗuwa.
20. A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
21. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
22. Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.
23. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
24. Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.
25. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
26. Dukkan wanda ke kanta ( 1 ) mai ƙãrẽwa ne.
27. Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
28. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
29. wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa ( Allah ) , a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.
30. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
31. Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ ( 2 ) mãsu nauyin halitta biyu!
32. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
33. Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.
34. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
35. Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?
36. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
37. Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
38. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
39. To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.
40. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
( 1 ) Yanã nufin ƙasa.
( 2 ) Mutãne da aljannu.