Surah Ar-Rahman | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 533
Suratul Al-Rahman from 41 to 67
41. zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
42. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
43. Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
44. Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
45. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
46. Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
47. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
48. Mãsu rassan itãce.
49. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
50. A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.
51. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
52. A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.
53. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
54. Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.
55. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
56. A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
57. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
58. Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
59. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
60. Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? ( Ã'aha ) fãce kyautatãwa.
61. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
62. Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
63. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
64. Mãsu duhun inuwa.
65. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
66. A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.
67. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?