Hausa translation of the meaning Page No 534

Quran in Hausa Language - Page no 534 534

Suratul Al-Rahman from 68 to 16


68. A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
69. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
70. A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
71. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
72. Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
73. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
74. Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
75. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
76. Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
77. To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
78. Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.
Sũratul Wãƙi‘a
Tanã karantar da kasuwar mutãne uku, kõwane kashi da hanyarsa a rãyuwarsa da mutuwarsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Idan mai aukuwa ta auku.
2. Bãbu wani ( rai ) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
3. ( Ita ) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
4. Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
5. Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
6. Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
7. Kuma kun kasance nau'i uku.
8. Watau mazõwa dãma. ( 1 ) Mẽne ne mazõwa dãma?
9. Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
10. Da waɗanda suka tsẽre.Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
11. Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
12. A ckin Aljannar ni'ima.
13. Jama'a ne daga mutãnen farko. ( 2 )
14. Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
15. ( Sunã ) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
16. Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
( 1 ) Mazõwa dãma ko mãsu albarka waɗanda zã a baiwa takardunsu a dãma. Mazõwa hagu ko mãsu shu'umci waɗanda zã a baiwa takardunsu da hagu.
( 2 ) Jama'a daga mutãnen farko, sũ ne Annabãwan farko da kaɗan daga cikin mutãnen ƙarshe, shi ne Annabi Muhammadu, sallallãhu alaihi wa sallama. Bã a shiga cikin wannan kashi da aiki saidai da zãɓin Allah. Kuma an rufe ƙõfarsa. Bãbu sauran wani annabi wanda zai zo da wani addini sãbo a bãyan Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.