Hausa translation of the meaning Page No 546

Quran in Hausa Language - Page no 546 546

Suratul Al-Hashr from 4 to 9


4. Wannan dõmin lalle su, sun sãɓa wa Allah, da ManzonSa alhãli kuwa wanda ya sãɓa wa Allah, to, lalle Allah, Mai tsananin uƙũba ne.
5. Abin da kuka sãre na dabĩniya, kõ kuka bar ta tsaye a kan asallanta, to da iznin Allah ne, kuma dõmin Ya wulãkanta fasiƙai,
6. Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga ManzonSa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da ManzanninSa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
7. Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya ( 1 ) ( matafiyi ) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.
8. ( Ku yi mãmãki ) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da ManzonSa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.
9. Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu ( ga Musulunci ) kuma ( suka zãɓi ) ĩmãni, a gabãnin zuwansu, ( 2 ) sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
( 1 ) Ɗan hanya, shĩ ne matafiyin da guzuri ya ƙãre masa, yanã nẽman taimakon da zai mayar da shi garinsa.
( 2 ) Muhãjirĩna sun yi hijira zuwa Madĩna daga Makka kõ waɗansu wurãre. Ansar, su ne mutãnen Madĩna. Waɗannan sũ ne ya kamãta a yi mãmãkin yadda suka taimaki addini a lõkacin tsanani. Muhãjirina sun bar gidãjensu da dũyarsu sun yi hijira, Ansarai sun raba dũkiyarsu da gidãjensu da iyãlansu sun bai wa Muhãjirĩna dõmin taimakon addĩni.