Hausa translation of the meaning Page No 547

Quran in Hausa Language - Page no 547 547

Suratul Al-Hashr from 10 to 16


10. Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, « Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai. »
11. Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci ( 1 ) ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, « Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan? » Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne.
12. Lalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan, zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba.
13. Lalle kũ ne kuka fi bãyar da firgita a cikin zukãtansu bisa ga Allah, wannan kuwa dõmin sũ lalle waɗansu irin mutãne ne da bã su gãnẽwa.
14. Bã su iya yãƙar ku gabã ɗaya, fãce a cikin garũruwa mãsu gãnuwa da gãruna, kõ kuma daga bãyan katangu. Yãkinsu a tsãkaninsu mai tsanani ne, kanã zaton su a haɗe, alhãli kuwa zukãtansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle wasu irin mutane ne da bã su hankalta.
15. Kamar misãlin waɗanda ( 2 ) ke a gabãninsu, bã da daɗẽwa ba, sun ɗanɗani kũɗar al'amarinsu, kuma sunã da wata azãba mai raRaɗi.
16. Kamar misãlin Shaiɗan a lõkacin da yake cẽ wa mutum, « Ka kãfirta, » To, a lõkacin da ya kãfirta ɗin, ya ce ( masa ) : « Lalle bãbu ruwãna da kai. Lalle ni inã tsõron Allah Ubangijin halitta! »
( 1 ) Bãyan ya nũna yadda Allah ke taimakon mai binsa da taƙawa. Kuma yanã nũna yadda Yake tãɓar da mai binSa da munãfinci.
( 2 ) Kuraishãwa da aka kashe a Badar.