Surah As-Saff | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 551
Suratul Al-Mumtahanah from 12 to 5
12. Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya'a a kan bã zã su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma bã su kashe, ( 1 ) ya'yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa ( 2 ) a tsãkanin hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a, to, ka karɓi mubãya'arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
13. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku jiɓinci waɗansu mutãne ( 3 ) da Allah Ya yi hushi a kansu. Lalle sun yanke tsammãni daga ( rahamar ) Lãhira, kamar yadda kãfirai suka yanke tsammãni daga mazõwa ( 4 ) kaburbura.
Sũratuṣ Ṣaff
Tanã karantar da gaskiyar maganar watau kada aikin mutum ya sãɓã wa maganarsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah alhãli kuwa, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima.
2. Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Don me kuke faɗin abin dã ba ku aikatãwa?
3. Ya girma ga zama abin ƙyãma awurin Allah, ku faɗi abin da bã ku aikatãwa.
4. Lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka KalmarSa, a cikin safu kamar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna.
5. Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: « Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Al1ah ne zuwa gare ku? » To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai.
( 1 ) A zãmanin jãhiliyya sun kashe 'ya'yansu mãtã ta hanya uku, ɗaya sabõda bãkance na addini, na biyu sabõda tsõron talauci; sunã turbuɗe 'ya'ya mãtã a bãyan sun shekara shida, na uku sabõda kunyar haihuwar mace, sai uwa ta yi rãmi, idan ta haifi namiji ta bar shi, idan kuma ta haifi mace, sai ta tũra ta a cikin rãmin ta turbuɗe.
( 2 ) Sunã tsintar yãro su mayar da shi ɗansu, haka kuma maza na yin tabanni, watau mutum ya mai da ɗan wani nãsa kamar yadda har yanzu kãfirai nã yin sa.
( 3 ) Allah Ya yi hushi ga duk wanda ya sani kuma ya ƙi aiki da saninsa kamar Yahũdãwa da miyãgun Mãlamai.
( 4 ) Kãfirai ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, sabõda haka suke yanke ƙauna daga wandaya mutu.