Hausa translation of the meaning Page No 560

Quran in Hausa Language - Page no 560 560

Suratul Al-Tahrim from 1 to 7


Sũratut Taḥrĩm
Tanã karantar da yadda ake kyautata zamantakẽwa da iyãli.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka, ( 1 ) kanã nẽman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2. Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware ( 2 ) rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.
3. Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: « Wãne ne ya gaya maka wannan? » Ya ce: « Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini. »
4. Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã'iku a bãyan wancan, mataimaka ne.
5. Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure mafiya alhẽri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli'u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da 'yammãta.
6. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku ( 3 ) (
da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su.
7. Yã kũ waɗanda suka kãfirta ( 4 ) ! Kada ku kãwo wani uzuri a yau. Anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa kawai ne.
( 1 ) A cikin littãfin Buhãri an ruwaito daga A'isha, mãtarAnnabi, cẽwa Annabi, tsĩra da amincinAllah su tabbata a gareshi, yakan yi jinkiri a wajen Zainab bint Jahsh dõmin ya shã zuma a wurinta. Ta ce: « Sai na shirya, nĩ da Hafsah: Duk wadda Manzon Allah ya shiga daga gareshi a gareta daga garemu, ta ce masa, 'Ina jin wãrin tsimi daga gareka! Kã ci tsimi! To, sai Annabi ya shiga ga ɗayansu, ta ce masa: » Kã ci tsimi. « Ya ce: » A'isha! Nã shã zuma dai a wurin Zainab bint Jahsh, kuma ba zan kõma gareshi ba. « Asalin abin, Annabi, tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi,yã kasance yanã zagayãwa a gidãjen mãtansa a bãyan sallar la'asar dõmin ya gaishe su. To, sai ya sh ga ga Hafsah bãyan ya shiga ga Zainab, ta gaya masa haka. Kuma ya gaya mata nĩsantarsa ga zuma, kuma ya gaya mata lãbãrin cẽwa Abubakar da Umar, Allah Ya yarda da su, za su zama halĩfai a bãyansa. To, sai ta faɗi waɗannan lãbãru ga maƙwabciyarta A'isha. Wannan Ƙissa tana koyar da sauƙin halin Annabi a game da iyãlansa, da girmamawarsa a gare su. »
( 2 ) An rubũta yadda ake warware rantsuwa da kaffãra wadda aka ambata a cikin sũra ta5, ãyã ta 89. Anã kaffãrar rantsuwa da ciyar da miskĩnai gõma daga matsakaicin abinci, mũdu biyu ga kõwane, kõ tufãtar da su tufar da za ta ishe su salla, idan bai sãmu ba, ya yi azumin kwãna uku.
( 3 ) Tsare kai da iyãli daga wuta yanã sãmuwa da shiryar da su da karãtu da nasiha a kan addini. Wannan yanã a cikin kyaun zamantakẽwa wanda sũrar ke karantarwa.
( 4 ) Kãfirai a nan, kafircinsu sabõda ƙin bin umurnin Allah game da kyaun zamantakewa da iyũli yake. Laifinsu yã fi sauran laifuffuka dõmin yanã sabbaba yãmutsi a gida, har abinya shãfi zurriya da ƙasã gabã ɗaya.