Hausa translation of the meaning Page No 563

Quran in Hausa Language - Page no 563 563

Suratul Al-Mulk from 13 to 26


13. Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, ( Allah ) , Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.
14. Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa?
15. Shi, ( Allah ) , Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake.
16. Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza?
17. Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda ( ãƙibar ) gargaɗiNa take.
18. Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata ( manzanni ) . To, yãya ( ãƙibar ) gargaɗiNa ta kasance?
19. Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai ( Allah ) , Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.
20. Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã ( Allah ) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu.
21. Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan ( Allah ) Ya riƙe arzikinSa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali.
22. Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya?
23. Ka ce: « ( Allah ) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku! »
24. Kuma kace « Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gareShi ne ake tãshin ku. »
25. Kuma sunã cewa, « Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ? »
26. Ka ce: « Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana ( gargaɗin ) . »