Hausa translation of the meaning Page No 562

Quran in Hausa Language - Page no 562 562

Suratul Al-Mulk from 1 to 12


Sũratul Mulk
Tanã karantar da tauhĩdi da kaɗaitar Allah ga mulki da halittawa da ni’imtawa da cikakken iko wanda yake tãre da rahama da tausayi.
ANA SON KARATUNTA DARE DUKA DA KUMA HARDACE TA DA KÃ.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. ( Allah ) , Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome.
2. Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.
3. Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar ( Allah ) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?
4. Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã.
5. Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr.
6. Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu.
7. Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa.
8. Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, « Wani mai gargaɗi bai je muku ba? »
9. Sai su ce: « I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.' »
10. Kuma suka ce: « Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba. »
11. Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr!
12. Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma.