Hausa translation of the meaning Page No 564

Quran in Hausa Language - Page no 564 564

Suratul Al-Mulk from 27 to 15


27. To, lokacin da suka gan ta ( azãbar ) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce ( musu ) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa.
28. Ka ce musu « Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi? »
29. Ka ce: « Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya. »
30. Ka ce: « Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga? » ( 1 )
Sũratul Ƙalam
Tanã yi wa Annabi bushara da cẽwa mutãnensa na Makka zã su shiga Musulunci, su yi nadãma a kan aikinsu na kãfirci da cutar da suka yi masa, kuma Allah zai karɓi tũbarsu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da ( marubũta ) suke rubũtãwa.
2. Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
3. Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
4. Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
5. Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
6. Ga wanenku haukã take.
7. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
8. Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
9. Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
10. Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
11. Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
12. Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
13. Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi ( bã ya son alhẽri ) .
14. Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
15. Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: « Tatsũniyõyin mutãnen farko ne. »
( 1 ) Ana so idan mai karatu ya kai ƙarshen wannan sũra ya ce:wato Allah Ubagijin halitta. An karanta wannan ãya a gaban wani kãfiri, sai ya ce zã mu fito da ruwan game da amfãni da dundurũsai da farẽtani, sai ruwan idãnunsa ya faƙe.