Hausa translation of the meaning Page No 575

Quran in Hausa Language - Page no 2 2

Suratul Al-Muzammil from 20 to 17


20. Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici ( daga wanda kuka ajiye ) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Sũratul Muddatthir
Tana karantar da fãra yin wa’azi ga dangi na kusa ga mai wa’azi kãmin ya fita zuwa ga wasu mutãne na nẽsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
2. Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
3. Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
4. Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
5. Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
6. Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
7. Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
8. To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
9. To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
10. A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
11. Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
12. Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
13. Da ɗiyã halartattu,
14. Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
15. Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
16. Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.
17. Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.