Hausa translation of the meaning Page No 574

Quran in Hausa Language - Page no 574 574

Suratul Al-Muzammil from 1 to 19


Sũratul Muzzammil
Tana karantar da tarbiyya da juriya ga Musulmi, dõmin susãmi dãmar tsayuwa da umurnin Allah.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Yã wanda ya lulluɓe!
2. Ka tsayu domin yin salla a cikin dare ( duka ) fãce kaɗan.
3. Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.
4. Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.
5. Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.
6. Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.
7. Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.
8. Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke ( ƙauna daga kowa ka koma ) zuwa gare Shi, yankewa.
9. Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili.
10. Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.
11. Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.
12. Lalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.
13. Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.
14. Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.
15. Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo ( 1 ) mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo ( 2 ) zuwaga Fir'auna,
16. Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.
17. To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre ( azabar ) wani yini mai mayar da yãra ( tsofaffi ) mãsu hurhura.
18. Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.
19. Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.
( 1 ) Wato Annabi Muhammad, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.
( 2 ) Wato Annabi Mũsã, aminci ya tabbata a gare shi.