Hausa translation of the meaning Page No 577

Quran in Hausa Language - Page no 577 577

Suratul Al-Muddaththir from 48 to 19


48. Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
49. Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.
50. Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
51. Sun gudu daga zãki.
52. A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu ( da sũnansa ) ana wãtsãwa
53. A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
54. A'aha! Lalle ne, shi ( Alƙur'ãni ) tunãtarwa ce.
55. Dõmin wanda ya so, ya tuna.
56. Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.
Sũratul Ƙiyãma
Tana karantar da bãyãnin yiwuwar Tãshin Ƙiyãma, da sifar mũmini ga saurin kãma umurnin Allah, da sakamakon wanda ya bi hanyar Allah, ko kuwa ya ƙi bin ta.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Bã sai Nã yi rantsuwa ( 1 ) da Rãnar Ƙiyãma ba.
2. Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin ( 2 ) kansa ba.
3. Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
4. Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
5. Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
6. Yanã tambaya: « Yaushe ne Rãnar Ƙiyãma? »
7. To, idan gani ya ɗimauta ( ya yi ƙyalli ) .
8. Kuma, watã ya yi husũfi ( haskensa ya dushe ) .
9. Aka tãra rãnã da watã
10. Mutum zai ce a rãn nan « Ina wurin gudu? »
11. A'aha! bãbu mafaka.
12. zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
13. Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
14. Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
15. Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa ( bã zã a saurãre shi ba ) .
16. Kada ka mõtsar ( 3 ) da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi ( Alƙur'ãni ) .
17. Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu ( tsare maka ) karãtunsa.
18. To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
19. sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
( 1 ) Wasu na fassarawa: lna rantsuwa da Rãnar Ƙiyama. A ganina, da tabbatar da rantsuwar da kuma kore ta duka ɗaya ne, maƙasũdi dai jan hankalin mai karãtu ga abin da yake a ciki, na hikimar Allah.
( 2 ) Kowane rai na zargin kansa idan bai yi aikin alheri ba, ko kuma bai yi fiye da wanda ya yi ba, ko kuma bai aikata wanda ya fi kyãwo ba a lokacin aikinsa.
( 3 ) Dangantakar wannan ãya da ta sama da ita ita ce bambancin Annabi mai gaugawar karɓar umurnin Allah da ƙyamar kãfiri ga karɓarsa, da bayãnin sauƙaƙẽwar Allah ga mai bin umurninSa.